17 Yuli 2026 - 22:31
Source: ABNA24
Dakarun Hashdush-Sha'abi Sun Fara Aiwatar Da Shirin Ayyuka Na Musamman Don Ziyarar Arba'in

Ƙungiyar Hashdush -Sha'abi ta fara aiwatar da shirin ayyuka na musamman don gudanar da ziyarar Arba'in na Imam Husain (A.S), bisa ga umarnin Abdul Aziz al-Muhammadawi, shugaban kwamitin ƙungiyar, tare da tuntubar gwamnan Karbala.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Dakarun Hashdush Sha'abi na Iraki a yau Juma'a sun sanar da cewa sun fara aiwatar da shirin ayyuka na musamman don taron ziyarar Arba'in.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Iraki (WAA), a cikin sanarwar wannan ƙungiya ya kawo cewa, Ƙungiyar Al-Hashd Al-Sha'abi ta fara aiwatar da shirin ayyuka na musamman don ziyarar Arba'in na Imam Husain (A.S), bisa ga umarnin Abdul Aziz al-Muhammadawi, shugaban kwamitin ƙungiyar Hashdush-Sha'abi, tare da hadin gwiwar gwamnan Karbala.

Bisa ga wannan sanarwa, an tura injuna da ƙwararrun ma'aikata zuwa wuraren aiwatar da ayyuka a hanyoyi daban-daban na birnin Karbala mai tsarki, don gudanar da ayyukan tsaftacewa, shirya hanyoyi, tallafawa hukumomin ayyuka, da kuma samar da yanayi don bayar da ayyuka ga miliyoyin maziyartan Arba'in.

A ci gaban sanarwar ya zo: Wannan mataki yana cikin wani shirin ayyuka na gaba ɗaya, tare da tuntuba da hukumomin gwamnati, tsaro da ayyuka, kuma manufarsa ita ce bayar da mafi kyawun ayyuka, tallafawa ƙoƙarin gwamnatin lardin, da kuma tabbatar da gudanar da ziyarar Arba'in na Imam Husain (A.S) cikin nasara.

……………….

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha